Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 21:20-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Sa'ad da Ahab ya ga Iliya, sai ya ce masa, “Ka tarshe ni ko, maƙiyina?”Iliya ya amsa ya ce, “I, na tarshe ka, gama ka ba da kanka ga aikata mugunta a gaban Ubangiji.

21. Saboda haka Ubangiji ya ce maka, ‘Ga shi, zan kawo maka masifa, in shafe ka, in datse maka kowane ɗa namiji, bawa ko ɗa, a Isra'ila.

22. Zan sa gidanka ya zama kamar gidan Yerobowam ɗan Nebat, da gidan Ba'asha ɗan Ahija saboda ka sa ni in yi fushi, ka kuma sa mutanen Isra'ila suka yi zunubi.’

23. A kan Yezebel kuwa Ubangiji ya ce, ‘Karnuka za su cinye Yezebel a cikin Yezreyel.’

24. Duk wanda yake na Ahab da zai mutu a birni karnuka ne za su cinye shi, wanda kuma ya mutu a waje tsuntsaye ne za su cinye shi.”

25. Babu wani kamar Ahab da ya ba da kansa ga aikata mugunta a gaban Ubangiji. Matarsa, Yezebel, ita ce ta zuga shi.

26. Ya yi abar banƙyama ƙwarai, ya bi gumaka kamar yadda Amoriyawa suke yi, waɗanda Ubangiji ya kore su a gaban Isra'ilawa.

27. Da Ahab ya ji wannan magana, sai ya yage tufafinsa, ya sa na makoki, ya yi azumi, ya kwanta a tsummokin makoki, ya tashi yana tafiya a hankali.

28. Ubangiji ya yi magana da Iliya Batishbe ya ce,

29. “Ka ga yadda Ahab ya ƙasƙantar da kansa a gabana? Da yake ya ƙasƙantar da kansa a gabana, ba zan kawo masifar a zamaninsa ba, sai a zamanin ɗansa ne, zan kawo masifar a kan gidansa.”

Karanta cikakken babi 1 Sar 21