Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 21:10-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. A kuma sa 'yan iska guda biyu, su yi ta zarginsa, su riƙa cewa, ‘Nabot ya zagi Allah da sarki.’ Sa'an nan ku tafi da shi, ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu.”

11. Mutanen birnin kuwa, dattawa da fādawan da suke zaune a birnin suka yi yadda Yezebel ta sa su yi, kamar yadda aka rubuta a wasiƙun da ta aika musu.

12. Suka kuwa yi shelar azumi, suka sa Nabot a gaban jama'a. 'Yan iska guda biyu suka zauna kusa da shi, suka yi ta zarginsa a gaban jama'a, suna cewa, “Nabot ya zagi Allah da sarki.”

13. Sai suka fitar da shi daga cikin birni, suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu.

14. Sa'an nan suka aika wa Yezebel cewa, “An jajjefi Nabot, ya mutu.”

15. Nan da nan da Yezebel ta ji an jajjefi Nabot har ya mutu, sai ta ce wa Ahab, “Tashi, ka mallaki gonar inabin Nabot, wadda ya ƙi sayar maka, gama Nabot ba shi da rai, ya mutu.”

16. Da Ahab ya ji Nabo ya mutu, sai ya tashi ya gangara zuwa gonar inabin Nabot Bayezreyele don ya mai da ta tasa.

17. Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Iliya Batishbe,

18. “Tashi, ka tafi, ka sadu da Ahab, Sarkin Isra'ila, wanda yake a Samariya, ga shi can a gonar inabin Nabot inda ya tafi don ya mallake ta.

19. Ka faɗa masa, ni Ubangiji, na ce, ‘Ka kashe mutum, kana kuma ƙwace abin da ya mallaka?’ Ka faɗa masa ga abin da na faɗa, ‘A wurin da karnuka suka lashe jinin Nabot, a nan ne kuma karnuka za su lashe jininka.’ ”

Karanta cikakken babi 1 Sar 21