Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 20:32-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. Sai suka sa tufafin makoki, suka ɗaura igiyoyi a wuyansu, suka tafi wurin Sarkin Isra'ila, suka ce, “Baranka, Ben-hadad, yana roƙonka ka bar shi da rai.”Ahab kuwa ya amsa ya ce, “Har yanzu yana da rai? Ai, shi kamar ɗan'uwana ne.”

33. Da ma abin da fādawan suke so su ji ke nan, sai suka yi sauri, suka karɓi maganar a bakinsa, suka ce, “I, ɗan'uwanka, Ben-hadad.”Sarki Ahab ya ce musu, “Ku je ku kawo shi.” Ben-hadad kuwa ya zo wurinsa. Ahab ya sa ya shiga tare da shi cikin karusarsa.

34. Ben-hadad ya ce masa, “Biranen da tsohona ya ƙwace daga wurin tsohonka, zan mayar maka. Kai kuma za ka yi karauku a Dimashƙu kamar yadda tsohonka ya yi a Samariya.”Sai Ahab ya ce, “Zan bar ka, ka tafi a kan wannan sharaɗi.” Ya kuwa yi alkawari da shi, sa'an nan ya bar shi, ya tafi.

35. Ubangiji ya umarci wani daga cikin annabawa ya ce wa abokinsa bisa ga umarnin Ubangiji, “Ina roƙonka ka buge ni.” Abokinsa kuwa ya ƙi ya buge shi.

Karanta cikakken babi 1 Sar 20