Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 2:42-46 Littafi Mai Tsarki (HAU)

42. sai ya aika a kirawo Shimai, ya ce masa, “Ashe, ban sa ka ka rantse da Ubangiji ba, na kuma dokace ka da ƙarfi, cewa ka tabbata ran da ka fita zuwa ko'ina za ka mutu? Kai kuma ka ce mini, ‘Abin da ka ce daidai ne, zan yi biyayya.’

43. To, me ya sa ka karya rantsuwar da ka yi da sunan Ubangiji, da kuma umarnin da na umarce ka?”

44. Sarki kuma ya ce masa, “Ka sani sarai irin duk muguntar da ka yi wa tsohona, Dawuda. Haka kuma Ubangiji zai sāka maka bisa ga muguntarka.

45. Amma Ubangiji zai sa mini albarka, ya kuma tabbatar da gadon sarautar Dawuda har abada.”

46. Sa'an nan sarki ya umarci Benaiya ɗan Yehoyada, ya tafi, ya kashe Shimai. Yanzu sarauta ta tabbata a hannun Sulemanu.

Karanta cikakken babi 1 Sar 2