Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 2:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'ad da lokacin rasuwar Dawuda ya gabato, sai ya yi wa ɗansa Sulemanu gargaɗi na ƙarshe, ya ce,

2. “Ina gab da rasuwa yanzu. Saboda haka, ka ƙarfafa, ka yi jaruntaka.

3. Ka yi abin da Ubangiji Allahnka ya umarce ka. Ka yi biyayya da dokokinsa, da umarnansa, kamar yadda aka rubuta a dokokin Musa, domin ka yi nasara da dukan abin da kake yi da inda ka nufa duka,

4. domin Ubangiji ya cika maganar da ya faɗa mini cewa, ‘Idan 'ya'yanka suna lura da hanyarsu, sun yi tafiya a gabana da gaskiya da zuciya ɗaya, da dukan ransu, ba za ka rasa mutum wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba.’

5. “Ka kuma san abin da Yowab ɗan Zeruya ya yi mini, yadda ya kashe shugabannin sojoji na Isra'ila su biyu, wato Abner ɗan Ner, da Amasa ɗan Yeter. Ya zubar da jinin yaƙi a lokacin salama. Ya sa jinin yaƙi a kan ɗamararsa wadda take gindinsa, da kuma kan takalmansa da yake ƙafafunsa.

6. Ka san abin da za ka yi, kada ka bar shi ya mutu ta hanyar lafiya.

7. “Amma ka nuna alheri ga 'ya'yan Barzillai daga Gileyad, ka lura da su da kyau, gama sun nuna mini alheri sa'ad da nake gudu daga ɗan'uwanka, Absalom.

8. “Ga kuma Shimai ɗan Gera, daga garin Bahurim ta Biliyaminu. Shi ne ya yi mini mugun zagi sa'ad da na tafi Mahanayim, amma sa'ad da ya zo taryata a Urdun, sai na rantse masa da Ubangiji, na ce ba zan kashe shi ba.

Karanta cikakken babi 1 Sar 2