Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 19:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ahab kuwa ya faɗa wa Yezebel dukan abin da Iliya ya yi, da yadda ya karkashe annabawan Ba'al duka.

2. Sai Yezebel ta aike a wurin Iliya ta ce, “Idan gobe war haka, ban kashe ka ba kamar yadda ka karkashe annabawan nan, to, alloli su hukunta ni.”

3. Sai Iliya ya ji tsoro, ya tashi, ya tsere zuwa Biyer-sheba ta Yahuza.Ya bar baransa a can.

4. Iliya ya yi tafiyarsa yini guda cikin jeji, ya tafi ya zauna a gindin wani itace ya yi roƙo domin ya mutu, yana cewa, “Yanzu ya isa haka, ya Ubangiji, ka karɓi raina, gama ban fi kakannina ba.”

5. Iliya kuwa ya kwanta, ya yi ta barci a gindin itacen. Farat sai mala'ika ya taba shi, ya ce masa, “Tashi, ka ci abinci.”

6. Da ya duba, sai ga waina da zafinta a bisa duwatsu, da butar ruwa a waje ɗaya. Ya ci, ya sha, ya koma kwantawa.

7. Mala'ikan Ubangiji kuma ya sake zuwa sau na biyu, ya taɓa shi, ya ce, “Tashi, ka ci abinci, in ba haka ba kuwa tafiya za ta gagare ka.”

8. Sai Iliya ya tashi ya ci abinci ya sha ruwa ya sami ƙarfi, sa'an nan ya kama tafiya kwana arba'in dare da rana har zuwa Horeb, wato dutsen Allah.

Karanta cikakken babi 1 Sar 19