Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 18:44-46 Littafi Mai Tsarki (HAU)

44. A zuwa na bakwai sai ya ce, “Na ga wani ɗan girgije kamar tafin hannu yana tasowa daga teku.”Iliya kuma ya ce, “Tafi, ka faɗa wa Ahab ya shirya karusarsa ya sauka don kada ruwan sama ya hana shi sauka.”

45. Jim kaɗan sai sararin sama ya yi baƙi ƙirin da gizagizai da iska, aka yi ruwan sama mai yawan gaske. Ahab kuwa ya hau karusarsa ya tafi Yezreyel.

46. Ubangiji kuwa ya saukar wa Iliya da iko, ya sha ɗamara, ya sheka a guje, ya riga Ahab isa Yezreyel.

Karanta cikakken babi 1 Sar 18