Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 18:24-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Za ku yi kira ga sunan Ba'al naku, ni kuma zan kira ga sunan Ubangiji. Allahn da ya amsa da wuta, shi ne Allah.”Jama'a duka suka yi sowar nuna yarda da wannan.

25. Sa'an nan Iliya ya ce wa annabawan Ba'al, “Ku zaɓi bijimi guda, ku shirya shi da farko, gama kuna da yawa, sa'an nan ku yi kira ga sunan Ba'al ɗinku, amma fa kada ku kunna wuta. ”

26. Suka kuwa kama bijimin da aka ba su, suka gyara shi suka yi ta kira ga sunan Ba'al tun da safe, har tsakar ranar suna ta cewa, “Ya Ba'al, ka amsa mana!” Amma ba murya, ba kuwa wanda ya amsa. Suka yi ta tsalle a wajen bagaden da suka gina.

27. Da rana ta yi tsaka sai Iliya ya yi musu ba'a, ya ce musu, “Ku kira da babbar murya, gama shi wani allah ne, watakila yana tunani ne, ko kuwa ya zagaya ne, ko kuma ya yi tafiya. Watakila kuma yana barci ne, sai a tashe shi.”

28. Suka yi ta kira da ƙarfi bisa ga al'adarsu, suna kuma tsattsaga jikunansu da wuƙaƙe, jini yana ta zuba.

29. Suka yi ta sambatu har azahar, lokacin ba da hadaya, amma ba muryar kowa, ba amsa, ba wanda ya kula.

30. Sa'an nan Iliya ya ce wa jama'a duka su zo kusa da shi. Jama'a duka kuwa suka zo kusa da shi. Sai ya gyara bagaden Ubangiji wanda aka lalatar.

31. Ya ɗibi duwatsu goma sha biyu bisa ga yawan kabilan 'ya'yan Yakubu, wanda Ubangiji ya ce masa, “Za a kira sunanka Isra'ila.”

32. Ya kuwa gina bagade da duwatsun da sunan Ubangiji. Ya kuma haƙa wuriya kewaye da bagaden, za ta ci kamar misalin garwar ruwa guda.

Karanta cikakken babi 1 Sar 18