Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 16:10-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. sai Zimri ya shiga gidan, ya buge shi ya kashe shi. Wannan ya faru a shekara ta ashirin da bakwai ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza.

11. Da Zimri ya zama sarki, nan da nan sai ya kashe dukan mutanen gidan Ba'asha, bai bar masa wani namiji, ko dangi, ko aboki ba.

12. Haka Zimri ya hallaka gidan Ba'asha bisa ga maganar da Ubangiji ya faɗa a kansa ta bakin annabi Yehu.

13. Wannan kuwa ya faru saboda zunuban Ba'asha da na ɗansa Ila, da zunuban da suka sa jama'ar Isra'ila su yi, har suka sa Ubangiji Allah na Isra'ila ya yi fushi saboda gumakansu.

14. Sauran ayyukan Ila da dukan abin da ya yi an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.

15. A shekara ta ashirin da bakwai ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Zimri ya yi sarauta kwana bakwai a Tirza. A lokacin nan sojoji suka kai wa Gibbeton ta Filistiyawa yaƙi.

16. Da sojojin da suke bakin dāga suka ji an ce Zimri ya shirya makirci, ya kashe sarki, sai dukan Isra'ilawa suka naɗa Omri, shugaban sojojin, can a sansani. A wannan rana ya zama Sarkin Isra'ila.

17. Omri kuwa ya tashi daga Gibbeton tare da dukan Isra'ila, suka kai wa Tirza yaƙi.

18. Da Zimri ya ga an ci birnin, sai ya tafi ya shiga hasumiyar da take a fāda, ya sa wa fādar wuta, wutar kuwa ta ƙone shi ya mutu.

Karanta cikakken babi 1 Sar 16