Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 16:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya yi magana da Yehu, ɗan Hanani a kan Ba'asha, ya ce,

2. “Tun da yake na ɗauke ka daga cikin ƙura, na maishe ka shugaban jama'ata Isra'ila, kai kuwa ka bi hanyar Yerobowam, ka sa jama'ata, wato Isra'ila, su yi zunubi, suka sa na yi fushi saboda zunubansu,

3. to, zan shafe ka da gidansa, in mai da gidanka kamar gidan Yerobowam ɗan Nebat.

4. Duk mutumin da yake naka da zai mutu a cikin birni, karnuka ne za su cinye shi. Wanda kuma ya mutu a saura, tsuntsaye ne za su cinye shi.”

5. Sauran ayyukan Ba'asha, da dukan abin da ya yi, da irin ƙarfinsa, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.

6. Ba'asha kuwa ya rasu, aka binne shi a Tirza. Sai Ila, ɗansa ya gāji sarautarsa.

7. Ubangiji kuma ya yi magana da Yehu ɗan Hanani, a kan Ba'asha da gidansa, saboda muguntar da ya aikata a gaban Ubangiji, har ya sa Ubangiji ya yi fushi, gama abin da ya aikata ya yi daidai da na Yerobowam, saboda kuma ya hallaka gidan Yerobowam.

8. A shekara ta ashirin da shida ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Ila ɗan Ba'asha, ya ci sarautar Isra'ila a Tirza. Ya yi sarauta shekara biyu.

9. Amma Zimri, shugaban rabin karusan Ila, ya yi masa maƙarƙashiya. Sa'ad da Ila yake Tirza, ya sha, ya bugu a gidan Arza wanda yake lura da fāda,

10. sai Zimri ya shiga gidan, ya buge shi ya kashe shi. Wannan ya faru a shekara ta ashirin da bakwai ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza.

11. Da Zimri ya zama sarki, nan da nan sai ya kashe dukan mutanen gidan Ba'asha, bai bar masa wani namiji, ko dangi, ko aboki ba.

12. Haka Zimri ya hallaka gidan Ba'asha bisa ga maganar da Ubangiji ya faɗa a kansa ta bakin annabi Yehu.

13. Wannan kuwa ya faru saboda zunuban Ba'asha da na ɗansa Ila, da zunuban da suka sa jama'ar Isra'ila su yi, har suka sa Ubangiji Allah na Isra'ila ya yi fushi saboda gumakansu.

14. Sauran ayyukan Ila da dukan abin da ya yi an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.

15. A shekara ta ashirin da bakwai ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Zimri ya yi sarauta kwana bakwai a Tirza. A lokacin nan sojoji suka kai wa Gibbeton ta Filistiyawa yaƙi.

Karanta cikakken babi 1 Sar 16