Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 15:5-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. domin Dawuda ya aikata abu mai kyau a gaban Ubangiji. Bai ƙetare umarnin da Ubangiji ya ba shi ba dukan kwanakin ransa, sai dai a kan Uriya Bahitte.

6. Akwai yaƙi tsakanin Abaija da Yerobowam dukan kwanakin ransa.

7. Sauran ayyukan Abaija da dukan abin da ya aikata, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

8. Abaija ya rasu, suka binne shi a Urushalima. Ɗansa Asa ya gāji sarautarsa.

9. A cikin shekara ta ashirin ta sarautar Yerobowam Sarkin Isra'ila, Asa ya sarauci jama'ar Yahuza.

10. Ya yi shekara arba'in da ɗaya yana sarauta a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Ma'aka, 'yar Absalom, wato kakarsa.

11. Asa kuwa ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda kakansa, Dawuda, ya yi.

12. Ya kori mata da maza da suke karuwanci a wuraren tsafi na arna a ƙasar, ya kuma kawar da gumakan da kakanninsa suka yi.

13. Ya kuma fitar da tsohuwarsa Ma'aka daga zaman sarauniya, domin ta yi ƙazantacciyar siffa ta gunkiyar Ashtoret. Asa ya sassare siffar, ya ƙone ta a rafin Kidron.

14. Amma ba a kawar da wuraren tsafi na tuddai ba, duk da haka Asa ya yi aminci sosai ga Ubangiji dukan kwanakinsa.

15. Ya kawo dukan tsarkakakkun abubuwan da tsohonsa ya keɓe, da kuma azurfa, da zinariya, da kwanoni waɗanda shi kansa ya yi, a cikin Haikalin Ubangiji.

16. Aka yi ta yaƙi tsakanin Asa da Ba'asha, Sarkin Isra'ila a dukan kwanakin mulkinsu.

17. Ba'asha, Sarkin Isra'ila, ya kai wa Yahuza yaƙi. Sai ya gina Rama don ya hana kowa ya fita ko kuma ya shiga wurin Asa, Sarkin Yahuza.

18. Sa'an nan Asa ya kwashe dukan azurfa da zinariya da suka ragu a ɗakunan ajiya na Haikalin Ubangiji, da na gidan sarki, ya ba barorinsa su kai wa Ben-hadad ɗan Tabrimmon, ɗan Heziyon, Sarkin Suriya, wanda yake zaune a Dimashƙu, ya ce,

19. “Bari mu ƙulla alkawari da juna kamar yadda tsohona da tsohonka suka yi, ga shi, na aika maka da kyautar azurfa da zinariya. Sai ka tafi, ka warware alkawarinka da Ba'asha, Sarkin Isra'ila, domin ya tashi ya bar ni.”

Karanta cikakken babi 1 Sar 15