Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 15:27-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Ba'asha ɗan Ahija kuwa daga gidan Issaka ya yi wa Nadab maƙarƙashiya, ya kashe shi a Gibbeton ta Filistiyawa, gama Nadab da mutanen Isra'ila sun kewaye Gibbeton da yaƙi.

28. Haka Ba'asha ya kashe Nadab a shekara ta uku ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, ya kuwa ci sarautar a maimakonsa.

29. Nan da nan da ya zama sarki, sai ya kashe dukan mutanen gidan Yerobowam, bai bar wani na gidan Yerobowam da rai ba, ya hallaka su sarai, bisa ga maganar Ubangiji wadda ya faɗa wa bawansa Ahija mutumin Shilo.

30. Wannan abu ya faru saboda zunubin Yerobowam da zunubin da ya sa mutanen Isra'ila su yi, ya tsokani fushin Ubangiji Allah na Isra'ila.

31. Sauran ayyukan Nadab, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.

32. Aka yi ta yaƙi tsakanin Asa Sarkin Yahuza, da Ba'asha Sarkin Isra'ila dukan kwanakin sarautarsu.

33. A cikin shekara ta uku ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Ba'asha ɗan Ahija ya yi sarautar Isra'ila a Tirza. Ya yi shekara ashirin da huɗu yana sarauta.

34. Ya aikata zunubi a gaban Ubangiji. Ya bi hanyar Yerobowam da zunubin da ya sa mutanen Isra'ila su yi.

Karanta cikakken babi 1 Sar 15