Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 13:7-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Sa'an nan sarkin ya ce wa annabin, “Zo mu tafi gida don ka shaƙata, zan ba ka lada.”

8. Annabin kuwa ya ce wa sarki, “Ko da za ka ba ni rabin gidanka, ba zan tafi tare da kai ba, ba kuma zan ci abinci ko in sha ruwa a wurin nan ba.

9. Gama Ubangiji ya umarce ni da cewa kada in ci abinci, ko in sha ruwa, ko in koma ta hanyar da na zo.”

10. Haka kuwa ya koma ta wata hanya dabam bai koma ta hanyar da ya bi zuwa Betel ba.

11. Akwai wani tsohon annabi a Betel. 'Ya'yansa maza kuwa suka tafi suka faɗa masa dukan abin da annabin Allah ya yi a Betel a wannan rana. Suka faɗa wa mahaifinsu maganar da annabin Allah ya faɗa wa sarki.

12. Tsohon annabin ya tambaye su, “Wace hanya ya bi?” Su kuwa suka nuna masa hanyar.

13. Ya ce musu su ɗaura wa jakinsa shimfiɗa. Sai suka ɗaura wa jakin shimfiɗa, shi kuwa ya hau,

14. ya bi bayan annabin nan da ya fito daga Yahuza, ya same shi yana zaune a gindin itace oak. Ya tambaye shi, “Ko kai ne annabin da ya zo daga Yahuza?”Mutumin ya amsa, “I, ni ne,”

15. Sa'an nan ya ce masa, “Zo mu tafi gida ka ci abinci.”

16. Amma annabin ya ce, “Ba zan koma tare da kai ba, ba kuwa zan shiga gida ba, ko in ci abinci, ko in sha ruwa tare da kai a wannan wuri,

17. gama Ubangiji ya ce mini kada in ci abinci, ko in sha ruwa a can, ko in koma ta hanyar da na zo.”

18. Sa,an nan tsohon annabin ya ce masa, “Ai, ni ma annabi ne kamarka. Ubangiji ya yi mini magana ta bakin wani mala'ika, ya ce mini in komar da kai gidana don ka ci abinci, ka sha ruwa.” Amma ƙarya ce ya yi masa.

Karanta cikakken babi 1 Sar 13