Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 13:19-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Saboda haka sai annabin ya koma tare da shi, ya ci abinci, ya sha ruwa a gidan tsohon annabin.

20. Sa'ad da suke zaune wurin ci, sai maganar Ubangiji ta zo ga tsohon annabin da ya komar da annabin Allah,

21. sai ya kira annabin Allah, wanda ya zo daga Yahuza, ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Da yake ba ka yi biyayya da maganar Ubangiji ba, ba ka kuma kiyaye umarnin da Ubangiji Allahnka ya umarce ka da shi ba,

22. amma ka komo, ka ci abinci, ka sha ruwa a wurin da ya ce maka, kada ka ci abinci, ko kuwa ka sha ruwa, saboda haka ba za a binne gawarka a kabarin kakanninka ba.’ ”

23. Bayan da ya ci abinci, ya sha sai tsohon annabin ya ɗaura wa jaki shimfiɗa don annabin da ya komo da shi.

24. Sa'ad da annabin Allah ya tafi, sai zaki ya gamu da shi a hanya, ya kashe shi, ya jefar da gawarsa a kan hanya. Sai jakin da zakin suka tsaya kusa da gawar.

25. Mutane suka wuce, suka ga gawar a kan hanya, da zaki a tsaye kusa da gawar. Suka tafi suka faɗa a birni, inda tsohon annabin nan yake.

26. Sa'ad da tsohon annabin nan ya ji, sai ya ce, “Wannan annabin Allah ne, wanda bai yi biyayya da maganar Ubangiji ba, saboda haka Ubangiji ya bashe shi ga zaki ya yayyage shi, ya kashe shi, kamar yadda Ubangiji ya faɗa masa.”

27. Sa'an nan ya ce wa 'ya'yansa maza, “Ku ɗaura mini shimfiɗa.” Su kuwa suka ɗaura,

28. ya hau ya tafi, ya iske gawar a hanya. Jakin da zakin suna tsaye kusa da gawar. Zakin bai ci gawar ba, bai kuma fāɗa wa jakin ba.

29. Tsohon annabin kuwa ya ɗauki gawar ya ɗora bisa jakin, ya kawo ta cikin birni, wato Betel, don yin makoki da binnewa.

30. Ya binne gawar a kabarinsa, sa'an nan suka yi makoki suna cewa, “Kaito, dan'uwana!”

31. Bayan da ya binne shi, sai ya ce wa 'ya'yansa, “Sa'ad da na rasu, sai ku binne ni a kabarin da aka binne annabin nan. Ku ajiye gawata kusa da tasa.

32. Gama maganar Ubangiji da ya faɗa game da bagaden da yake cikin Betel, da masujadai na kan tuddai waɗanda suke a garuruwan Samariya, za ta cika.”

Karanta cikakken babi 1 Sar 13