Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 12:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Rehobowam ya tafi Shekem, gama dukan mutanen Isra'ila sun tafi Shekem don su naɗa shi sarki.

2. Sa'ad da Yerobowam, ɗan Nebat, ya ji labari, gama a lokacin yana Masar inda ya gudu saboda sarki Sulemanu, sai ya komo daga Masar.

3. Suka aika a kirawo shi, sai Yerobowam da dukan taron jama'ar Isra'ila suka zo suka ce wa Rehobowam,

4. “Tsohonka ya nawaita mana, yanzu sai ka rage mana wahalar aikin tsohonka da nawayarsa a kanmu, mu kuwa za mu bauta maka.”

5. Sai ya ce musu, “Ku tafi, ku sāke zuwa bayan kwana uku.” Sai suka tafi.

6. Sarki Rehobowam kuwa ya nemi shawara daga wurin dattawa, waɗanda suka bauta wa tsohonsa, Sulemanu, lokacin da yake da rai. Ya ce musu, “Wace shawara za ku ba ni don in amsa wa mutanen nan?”

7. Suka ce masa, “Idan za ka zama mai lura da jama'an nan yau, ka bauta musu, sai ka yi musu magana da kyau, su kuwa za su zama talakawanka har abada.”

Karanta cikakken babi 1 Sar 12