Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 10:23-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Sarki Sulemanu ya fi dukan sarakunan duniya dukiya da hikima.

24. Dukansu suna so su zo wurin Sulemanu don su ji hikimarsa wadda Allah ya ba shi.

25. Kowannensu yakan kawo masa yawan kyautai na kayayyakin azurfa, da na zinariya, da riguna, da turare, da kayan yaji, da dawakai, da alfadarai kowace shekara.

26. Sulemanu kuwa ya tattara karusai da mahayan dawakai. Yana da karusai dubu da ɗari huɗu (1,400), da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000), waɗanda ya zaunar da su a biranen karusai da kuma waɗansu tare da shi a Urushalima.

27. Sarki ya sa azurfa ta gama gari, kamar dai duwatsu a Urushalima, itacen al'ul kuma ya zama kamar jumaiza na Shefela.

28. Sulemanu kuwa ya sayo dawakai daga Masar da Kuye. 'Yan kasuwar sarki sukan sayo dawakai daga Kuye a kan tamaninsu.

29. Akan sayo karusa a Masar a bakin azurfa ɗari shida, doki kuwa a bakin ɗari da hamsin, 'yan kasuwar sarki sukan sayar da su ga dukan sarakunan Hittiyawa da na Suriyawa.

Karanta cikakken babi 1 Sar 10