Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sar 10:16-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Sarki Sulemanu ya yi manyan garkuwoyi guda ɗari biyu da zinariya. Anyi kowace garkuwa da shekel ɗari shida na zinariya.

17. Ya kuma yi waɗansu garkuwoyi guda ɗari uku da zinariya. An yi kowace garkuwa da shekel dari uku na zinariya. Sarki kuwa ya ajiye su a ɗakin da aka gina da katakai daga Lebanon.

18. Ya kuma yi babban gadon sarauta na hauren giwa, sa'an nan ya dalaye shi da tattacciyar zinariya.

19. Gadon sarautar yana da matakai shida da siffar kan maraƙi a bayan gadon sarautar, a kowane gefen mazaunin kuma, akwai wurin ɗora hannu da siffofin zaki biyu suna tsaye a gefen wuraren ɗora hannun.

20. Akwai siffar zaki goma sha biyu suna tsaye a kowane gefen matakan nan shida. Ba a taɓa yin irinsu a kowace masarauta ba.

21. Dukan finjalai na sarki Sulemanu, da zinariya aka yi su, haka kuma finjalan da suke cikin ɗakin da aka gina da katakai daga Lebanon, ba a yi wani finjali da azurfa ba, domin ba a mai da azurfa kome ba a kwanakin Sulemanu.

22. Gama sarki yana da rundunar jiragen ruwa a tekun Tarshish tare da na Hiram. Sau ɗaya a shekara uku rundunar jiragen ruwa na Tarshish sukan kawo zinariya, da azurfa, da hauren giwa, da birai, da ɗawusu masu daraja.

23. Sarki Sulemanu ya fi dukan sarakunan duniya dukiya da hikima.

24. Dukansu suna so su zo wurin Sulemanu don su ji hikimarsa wadda Allah ya ba shi.

25. Kowannensu yakan kawo masa yawan kyautai na kayayyakin azurfa, da na zinariya, da riguna, da turare, da kayan yaji, da dawakai, da alfadarai kowace shekara.

26. Sulemanu kuwa ya tattara karusai da mahayan dawakai. Yana da karusai dubu da ɗari huɗu (1,400), da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000), waɗanda ya zaunar da su a biranen karusai da kuma waɗansu tare da shi a Urushalima.

27. Sarki ya sa azurfa ta gama gari, kamar dai duwatsu a Urushalima, itacen al'ul kuma ya zama kamar jumaiza na Shefela.

Karanta cikakken babi 1 Sar 10