Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 6:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Akwatin alkawarin Ubangiji ya yi wata bakwai a ƙasar Filistiyawa.

2. Filistiyawa suka kirawo firistocinsu da bokayensu, suka ce, “Me za mu yi da akwatin alkawarin Ubangiji? Ku sanar da mu yadda za mu komar da shi inda ya fito.”

3. Sai firistocin da bokayen suka ce, “Idan za ku komar da akwatin alkawarin Allah na Isra'ila, dole ku aika da kyauta tare da shi domin zunubinku. Ba dama a komar da akwatin alkawarin hannu wofi. Ta haka za ku sami lafiya, za ku kuma san dalilin da ya sa ya yi ta hukunta ku.”

4. Suka ce, “Wace irin hadaya za mu bayar?”Firistocin suka ce, “Sai ku yi marurai biyar na zinariya da ɓeraye biyar na zinariya bisa ga yawan sarakunan Filistiyawa, gama annoba iri ɗaya ce ta same ku da sarakunanku.

5. Ku yi siffofin marurai da na ɓeraye waɗanda suka lalatar da ƙasar, ku ba da girma ga Allah na Isra'ila, watakila zai ɗauke hukuncinsa a kanku, da allolinku, da ƙasarku.

6. Don me za ku taurare zukatanku kamar yadda Masarawa da Fir'auna suka taurare zukatansu? Sai da Allah ya wahalshe su tukuna kafin su sallami Isra'ilawa su tafi.

7. Yanzu kuwa ku yi sabon keken shanu, ku sami shanun tatsa biyu waɗanda ba a taɓa sa musu karkiya ba, ku ɗaura wa shanun keken, amma ku tsare 'yan maruƙansu a gida.

8. Sa'an nan ku sa akwatin alkawarin Ubangiji a keken shanun, ku kuma sa siffofin maruran da na ɓerayen a cikin wani akwati ku ajiye a gefen akwatin alkawarin. Ku aika da waɗannan abubuwa tare da shi don yin hadaya ta laifi. Sa'an nan ku sa shi a hanya, a bar shi, ya tafi.

9. Ku zuba ido, ku gani, idan ya kama hanya zuwa Bet-shemesh, to, shi ne ya kawo mana wannan babbar masifa, amma idan ba haka ba, za mu sani ba shi ne ya buge mu ba, tsautsayi ne kawai.”

10. Suka yi yadda aka faɗa musu, suka sami shanun tatsa biyu, suka ɗaura musu karkiyar keken. Suka tsare 'yan maruƙansu a gida.

11. Suka sa akwatin alkawarin Ubangiji a keken, da akwatin siffofin ɓerayen zinariya da siffofin maruran.

12. Shanun kuwa suka kama hanya sosai wadda ta nufi wajen Bet-shemesh, suna tafe, suna ta kuka, ba su kauce zuwa dama ko hagu ba, sarakunan Filistiyawa suna biye da su, har zuwa iyakar Bet-shemesh.

Karanta cikakken babi 1 Sam 6