Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 29:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Filistiyawa suka tattara rundunar yaƙinsu a Afek. Isra'ilawa kuma suka kafa sansaninsu kusa da maɓuɓɓugar da take a Yezreyel.

2. Sa'ad da sarakunan Filistiyawa suke wucewa da rundunarsu na mutum ɗari ɗari da na mutum dubu dubu, Dawuda kuma da mutanensa suna biye a baya tare da Akish.

3. Shugabannin sojojin Filistiyawa suka ce, “Me waɗannan Ibraniyawa suke yi a nan?”Akish kuwa ya ce wa shugabannin sojojin Filistiyawa, “Ai, wannan Dawuda ne baran Saul, Sarkin Isra'ila, wanda yake tare da ni tun da daɗewa. Tun lokacin da ya zo wurina ban taɓa samunsa da wani laifi ba.”

4. Amma shugabannin sojojin Filistiyawa suka husata da shi, suka ce masa, “Ka sa mutumin nan ya koma wurin da ka zaunar da shi. Ba zai tafi tare da mu zuwa wurin yaƙin ba, don kada ya juya mana gindin baka. Ai, da kawunan mutanenmu ne zai yi sulhu da ubangijinsa.

Karanta cikakken babi 1 Sam 29