Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 28:9-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Matar ta ce masa, “Hakika ka san abin da sarki Saul ya yi, yadda ya karkashe masu duba da masu maita a ƙasar. Me ya sa kake ƙoƙarin kafa mini tarko, don ka sa a kashe ni?”

10. Saul ya rantse mata da Ubangiji, ya ce, “Hakika, ba za a hukunta ki saboda wannan ba.”

11. Sai matar ta ce, “Wa kake so in hawar maka?”Ya ce, “Ki hawar mini da Sama'ila.”

12. Da matar ta ga Sama'ila, sai ta fasa ƙara, ta ce wa Saul, “Don me ka ruɗe ni, ashe, kai ne sarki Saul?”

13. Sarki kuwa ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, me kike gani?”Ta ce masa, “Na ga wani allah yana fitowa daga ƙasa.”

14. Ya ce mata, “Yaya kamanninsa yake?”Ta ce, “Wani tsoho ne yake hawowa, yana naɗe da alkyabba.”Saul ya gane Sama'ila ne, sai ya sunkuyar da kai, ya durƙusa har ƙasa da bangirma.

15. Sai Sama'ila ya ce wa Saul, “Don me ka dame ni, ka hawar da ni?”Saul ya ce, “Ina cikin babbar wahala, gama Filistiyawa suna yaƙi da ni, Allah kuma ya rabu da ni, ya ƙi amsa mini ko ta wurin annabawa ko ta mafarkai, saboda haka na kira ka, ka faɗa mini abin da zan yi.”

16. Sai Sama'ila ya ce masa, “Don me za ka tambaye ni, tun da yake Ubangiji ya rabu da kai, ya zama magabcinka?

17. Ai, abin da Ubangiji ya faɗa mini a kanka, shi ne ya cika, gama Ubangiji ya fizge mulki daga hannunka, ya ba maƙwabcinka Dawuda.

18. Domin ba ka bi maganar Ubangiji ba, ba ka zartar da hukuncinsa mai zafi a kan Amalekawa ba, saboda haka Ubangiji ya yi maka haka yau.

19. Banda haka kuma Ubangiji zai ba da Isra'ilawa tare da kai a hannun Filistiyawa. Gobe, da kai da 'ya'yanka maza za ku kasance tare da ni. Ubangiji zai ba da rundunar yaƙin Isra'ila a hannun Filistiyawa.”

20. Da jin maganar Sama'ila sai Saul ya faɗi ƙasa warwar. Tsoro ya kama shi ƙwarai. Ba shi kuma da ƙarfi domin bai ci kome dukan yini da dukan dare ba.

Karanta cikakken babi 1 Sam 28