Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 25:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sama'ila kuwa ya rasu. Dukan Isra'ilawa suka taru suka yi makoki dominsa. Suka binne shi a gidansa a Rama.Sai Dawuda ya tashi ya tafi jejin Faran.

2. Akwai wani mutumin Mawon wanda yake da harka a Karmel. Mutumin mai dukiya ne ƙwarai, yana da tumaki dubu uku (3,000) da awaki dubu (1,000). Yana yi wa tumakinsa sausaya a Karmel.

3. Sunan mutumin kuwa Nabal, sunan matarsa kuma Abigail, ita haziƙa ce, kyakkyawa, amma mijinta miskili ne, marar mutunci. Shi daga zuriyar Kalibu ne.

4. Daga cikin jeji, Dawuda ya ji, wai Nabal yana yi wa tumakinsa sausaya,

5. sai ya aiki samari goma, ya ce musu, “Ku tafi Karmel wurin Nabal, ku ce ina gaishe shi.

6. Gaisuwar da za ku yi masa ke nan, ku ce, ‘Salama gare ka, salama ga gidanka, salama kuma ga dukan abin da kake da shi.

7. Na ji kana da masu sausaya. Lokacin da makiyayanka suke tare da mu, ba mu cuce su ba, ba abin da ya ɓace musu dukan lokacin da suke a Karmel.

8. Tambayi samarinka, za su faɗa maka. Saboda haka ka yarda samarina su sami tagomashi a wurinka, gama yau ranar biki ce. Muna roƙonka ka ba barorinka, da ɗanka, Dawuda abin da za ka iya ba mu.’ ”

9. Sa'ad da samarin Dawuda suka zo, suka faɗa wa Nabal dukan abin da Dawuda ya ce musu, sai suka dakata.

10. Nabal ya amsa wa barorin Dawuda, ya ce, “Wane ne Dawuda? Wane ne ɗan Yesse? A kwanakin nan akwai barori da yawa waɗanda suka tayar wa iyayengijinsu.

11. Zan ɗauki abincina, da ruwana, da namana wanda na yanka wa masu yi mini sausaya in ba mutanen da ban san inda suka fito ba?”

Karanta cikakken babi 1 Sam 25