Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 20:5-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Dawuda kuwa ya ce masa, “Ga shi, gobe ce amaryar wata, dole ne in zauna tare da sarki a teburinsa. Ka bar ni in tafi in ɓuya a saura har kwana uku.

6. Idan mahaifinka bai gan ni ba, sai ka ce masa, ni na roƙe ka ka bar ni in gaggauta zuwa Baitalami, garinmu, domin akwai ba da sadaka ta shekara saboda dukan gidanmu.

7. Idan ka ji ya ce, ‘Da kyau,’ to, baranka zai tsira ke nan, amma idan ya husata, to, sai ka sani yana niyyar kashe ni ke nan,

8. kai kuwa ka nuna mini alheri, gama ka yi mini alkawari mai ƙarfi. Amma idan ina da laifi, sai ka kashe ni da kanka. Don me za ka bar mahaifinka ya kashe ni?”

9. Jonatan ya masa ya ce, “Allah ya sawwaƙe! Da na sani babana yana da nufi ya yi maka mugunta, ai, da na faɗa maka.”

10. Sa'an nan Dawuda ya ce wa Jonatan, “Wane ne zai faɗa mini idan mahaifinka ya amsa maka da fushi?”

11. Jonatan kuwa ya ce masa, “Zo mu tafi saura.” Sai su biyu suka tafi saura.

12. Sa'an nan Jonatan ya ce wa Dawuda, “Ubangiji Allah na Isra'ila zai zama shaida. Gobe war haka, ko jibi zan tattauna maganar da mahaifina, idan da nufin alheri zuwa gare ka, zan aika, in faɗa maka.

13. Amma idan har mahaifina yana da niyyar yi maka mugunta, amma ban sanar da kai ba, to, bari Ubangiji ya hukunta ni. Ubangiji ya kasance tare da kai kamar yadda ya kasance da mahaifina.

14. Ba lokacin da nake da rai ne kaɗai za ka nuna mini alherin Ubangiji domin kada in mutu ba.

15. Ko bayan raina kada ka daina nuna wa gidana alheri har abada, lokacin da Ubangiji ya datse maƙiyanka daga fuskar duniya.”

16. Jonatan ya yi alkawari da gidan Dawuda. Ubangiji kuwa zai ɗauki fansa a kan maƙiyan Dawuda.

Karanta cikakken babi 1 Sam 20