Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 19:12-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Sai ta zurarar da Dawuda ta taga, ya gudu, ya tsere.

13. Mikal kuwa ta ɗauki kan gida ta kwantar da shi a gado, ta kuma sa masa matashin kai na gashin awaki, sa'an nan ta lulluɓe shi da mayafi.

14. Sa'ad da manzannin Saul suka zo don su kama Dawuda, sai ta ce musu, “Ba shi da lafiya.”

15. Saul kuma ya sāke aiken manzannin su tafi su ga Dawuda, ya ce musu, “Ku kawo shi nan wurina a kan gadonsa don in kashe shi.”

16. Da manzannin suka tafi, sai suka tarar da kan gida a gadon, da matashin kai na gashin awaki wajen kansa.

17. Saul kuwa ya ce wa Mikal, “Don me kika ruɗe ni har kika bar maƙiyina ya tsere?”Ta ce wa Saul, “Ya ce mini, idan ban bar shi ya tafi ba, zai kashe ni.”

18. Dawuda ya gudu, ya tsere zuwa wurin Sama'ila a Rama, ya faɗa masa dukan abin da Saul ya yi masa. Shi da Sama'ila suka tafi suka zauna a Nayot.

19. Aka faɗa wa Saul cewa, “Dawuda yana a Nayot ta Rama.”

20. Sai ya aika da manzanni su tafi su kama Dawuda. Da suka kai, suka iske ƙungiyar annabawa suna annabci, Sama'ila kuwa yana tsaye a gabansu. Ruhun Allah ya sauko a kan manzannin Saul, su kuma suka yi annabci.

21. Aka faɗa wa Saul, sai ya sāke aiken waɗansu, su kuma suka shiga yin annabci. Ya kuma sāke aiken manzanni aji na uku, su kuma suka shiga yin annabci.

22. Saul kuma ya tafi Rama da kansa. Da ya kai babbar rijiyar da suke a Seku, sai ya tambayi inda Sama'ila da Dawuda suke. Wani ya ce masa, “Suna Nayot ta Rama.”

23. Sai ya tashi daga can zuwa Nayot ta Rama. Ruhun Allah kuwa ya sauko a kansa, sai shi kuma ya shiga yin annabci har ya kai Nayot ta Rama,

24. ya kuma tuɓe tufafinsa, ya yi ta annabci a gaban Sama'ila. Ya kwanta huntu dukan yini da dukan dare. Don haka aka riƙa yin karin magana da cewa, “Har Saul ma yana cikin annabawa?”

Karanta cikakken babi 1 Sam 19