Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 17:43-52 Littafi Mai Tsarki (HAU)

43. Ya ce wa Dawuda, “Ni kare ne da za ka nufo da sanduna?” Ya zagi Dawuda da sunan allolinsu na Filistiyawa.

44. Ya kuma ce wa Dawuda, “Ya ka nan, ni kuwa in ba da namanka ga tsuntsayen sama da namomin jeji.”

45. Dawuda kuwa ya ce masa, “Kai, kana nufo ni da takobi, da mashi, da kēre, amma ni ina zuwa wurinka da sunan Ubangiji Mai Runduna, Allah na sojojin Isra'ila, wanda ka raina.

46. A yau Ubangiji zai bashe ka a hannuna, zan buge ka har ƙasa, in datse kanka, in ba da gawawwakin rundunar Filistiyawa ga tsuntsayen sama da namomin jeji, da haka duniya za ta sani lalle akwai Allah cikin Isra'ila.

47. Taron jama'ar nan kuma za su sani Ubangiji yakan yi ceto ba da takobi da mashi ba, gama yaƙi na Ubangiji ne, zai bashe ku a hannunmu.”

48. Goliyat kuwa ya fara gusowa ya gamu da Dawuda, sai Dawuda ya sheƙa zuwa bakin dāgar yaƙin don ya gamu da shi.

49. Sa'an nan Dawuda ya ɗauko dutse daga cikin angararsa, ya wurga, dutsen kuwa ya sami Goliyat a goshi, har ya lume. Goliyat kuwa ya faɗi rubda ciki.

50. Da majajjawa da dutse kawai Dawuda ya ci nasara da Bafilisten. Ya buge shi, ya kashe shi ba tare da takobi a hannunsa ba.

51. Sa'an nan ya sheƙa zuwa wurin Bafilisten, ya zare takobin Bafilisten daga kubensa, ya datse masa kai da shi.Da Filistiyawa suka ga jaruminsu ya mutu, sai suka gudu.

52. Mutanen Isra'ila da na Yahuza suka tashi suka runtumi Filistiyawa, suna ihu, har zuwa Gat da ƙofofin Ekron. Filistiyawan da aka yi wa rauni suka yi ta faɗuwa a hanya tun daga Shayarim, har zuwa Gat da Ekron.

Karanta cikakken babi 1 Sam 17