Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 17:25-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Suka ce, “Kun ga mutumin nan da ya fito? Lalle ya fito ne don ya nuna mana raini. Duk wanda ya kashe shi, sarki zai arzutar da shi, ya ba shi 'yarsa aure, ya kuma 'yantar da gidan mahaifinsa cikin Isra'ila.”

26. Sai Dawuda ya tambayi mutanen da suke kusa da shi, ya ce, “Me za a yi wa wanda ya kashe Bafilisten nan, har ya kawar da zargi daga Isra'ila? Gama wane ne wannan Bafiliste, marar kaciya, da zai raina rundunar Allah mai rai?”

27. Mutane suka maimaita masa abin da sarki ya faɗa.

28. Lokacin da Dawuda yake magana da mutanen, sai Eliyab babban wansa ya ji, ya husata, ya ce wa Dawuda, “Me ya kawo ka nan? Wa ka bar wa 'yan tumakin nan a jeji? Na san rigimarka da taurinkanka, ka zo ne don ka yi kallon yaƙi.”

29. Dawuda kuwa ya ce, “To, me kuma na yi, ba tambaya kawai na yi ba?”

30. Sai ya rabu da shi ya tafi wurin wani, ya sāke yin tambaya irin ta dā, mutane kuma suka ba shi amsa irin ta dā.

31. Sa'ad da waɗansu suka ji maganar da Dawuda ya yi, sai suka faɗa wa Saul. Shi kuwa ya aika a kira Dawuda.

32. Dawuda kuwa ya ce wa Saul, “Kada zuciyar kowa ta karai saboda wannan mutum, baranka zai tafi ya yi yaƙi da shi.”

Karanta cikakken babi 1 Sam 17