Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 17:12-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Dawuda kuwa ɗan Yesse ne, wanda yake mutumin Efrata, ta Baitalami cikin Yahuza, yana da 'ya'ya maza guda takwas, ya kuwa riga ya tsufa a zamanin Saul.

13. Manyan 'ya'yansa maza uku sun tafi yaƙi tare da Saul. Sunan babban ɗan, Eliyab, na biye da shi kuma, Abinadab, na ukun kuwa Shimeya.

14. Dawuda shi ne auta. Sa'ad da manyan 'yan'uwansa uku suka tafi tare da Saul wurin yaƙi,

15. Dawuda yakan koma Baitalami lokaci lokaci domin kiwon tumakin mahaifinsa.

16. Goliyat yana ta tsokanar Isra'ilawa safe da maraice, har kwana arba'in.

17. Wata rana ke nan, sai Yesse ya ce wa Dawuda, ɗansa, “Ka ɗauki wannan tumammen hatsi, da malmalar abinci goma, ka kai wa 'yan'uwanka da sauri a sansanin.

18. Ga waɗannan dunƙulen cuku goma, ka kai wa shugaba na mutum dubu. Ka dubo lafiyar 'yan'uwanka, ka kawo mini labari.

19. Da Saul, da 'yan'uwanka, da dukan mazajen Isra'ila suna kwarin Ila, suna yaƙi da Filistiyawa.”

20. Kashegari sai Dawuda ya tashi tun da sassafe, ya bar tumaki a hannun wani makiyayi, ya ɗauki guzurin, ya tafi kamar yadda mahaifinsa, Yesse, ya umarce shi. Ya isa sansani daidai lokacin da runduna suke fita tana kirari na jān dāgar yaƙi.

21. Isra'ilawa da Filistiyawa suka jā dāga, runduna gāba da runduna.

Karanta cikakken babi 1 Sam 17