Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 16:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce wa Sama'ila, “Har yaushe za ka yi ta ɓacin rai saboda Saul? Ga shi kuwa, na ƙi shi da zama Sarkin Isra'ila. Ka sami man zaitun ka ɗauka. Zan aike ka zuwa wurin Yesse mutumin Baitalami, gama na zaɓi ɗaya daga cikin 'ya'yansa maza ya zama sarki.”

2. Sama'ila kuwa ya ce, “Ƙaƙa zan yi wannan? Gama idan Saul ya ji zai kashe ni.”Sai Ubangiji ya ce, “Ka tafi da ɗan maraƙi, ka ce, ka zo ne ka miƙa wa Ubangiji hadaya.

3. Ka gayyaci Yesse zuwa wurin hadayar, zan nuna maka abin da za ka yi. Za ka zuba wa wanda na nuna maka mai.”

4. Sama'ila ya yi yadda Ubangiji ya faɗa masa, ya tafi Baitalami, inda dattawan garin suka tarye shi da rawar jiki, suka ce masa, “Maigani, wannan ziyara lafiya kuwa?”

5. Ya ce, “I, lafiya lau. Na zo ne in miƙa wa Ubangiji hadaya, sai ku tsarkake kanku, ku zo mu tafi wurin yin hadaya tare.” Ya kuma sa Yesse da 'ya'yansa maza su tsarkake kansu, su je wurin hadayar.

6. Da suka isa wurin hadayar, Sama'ila ya ga Eliyab, ɗan Yesse, sai ya zaci shi ne wanda Ubangiji ya zaɓa.

7. Amma Ubangiji ya ce masa, “Kada ka kula da kyan tsarinsa, ko tsayinsa, domin ba shi nake so ba, gama yadda Ubangiji yake gani, ba haka mutum yake gani ba. Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai, amma Ubangiji yakan dubi zuciya.”

Karanta cikakken babi 1 Sam 16