Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 15:6-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ya ce wa Keniyawa, “Ku tafi, ku rabu da Amalekawa, don kada in hallaka ku tare da su, gama kun yi wa dukan Isra'ilawa karamci lokacin da suka fito daga Masar.” Keniyawa kuwa suka fita daga cikin Amalekawa.

7. Saul ya ci Amalekawa, tun daga Hawila har zuwa Shur, da yake gabashin Masar,

8. ya kama Agag Sarkin Amalekawa da rai, ya hallaka mutane ƙaƙaf da takobi.

9. Amma Saul da jama'arsa suka bar Agag da rai, ba su kuma kashe tumaki da takarkarai mafi kyau ba, da 'yan maruƙa, da raguna, da dukan abin da yake mai kyau, bai yarda su hallaka su duka ba, amma sun hallaka dukan abin da yake rainanne ko marar amfani.

10-11. Sai Ubangiji ya yi magana da Sama'ila ya ce, “Na yi baƙin ciki da na sa Saul ya zama sarki, gama ya rabu da ni, ya yi rashin biyayya ga umarnaina,” Sama'ila kuwa ya yi fushi, ya yi ta roƙo ga Ubangiji dukan dare.

12. Sa'an nan ya tashi tun da sassafe domin ya sadu da Saul. Aka faɗa wa Sama'ila, Saul ya tafi Karmel, ya kafa wa kansa al'amudi, sa'an nan ya juya ya wuce zuwa Gilgal.

13. Sai Sama'ila ya tafi wurin Saul, Saul kuwa ya gaishe shi, ya ce, “Ubangiji ya sa maka albarka, Sama'ila, na yi biyayya ga umarninsa.”

14. Sama'ila ya ce masa, “To, ina baicin wannan kukan shanu da na tumaki da nake ji?”

15. Saul kuwa ya ce, “Ai, mutanena ne suka kawo su daga Amalekawa. Gama sun bar mafi kyau na tumaki, da na shanu domin su miƙa su sadaka ga Ubangiji Allahnka. Mun hallaka sauran ƙaƙaf.”

16. Sa'an nan Sama'ila ya ce wa Saul, “Dakata, in faɗa maka abin da Ubangiji ya faɗa mini a daren jiya.” Sai Saul ya ce, “Faɗa mini.”

Karanta cikakken babi 1 Sam 15