Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 15:27-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Sa'an nan Sama'ila ya juya zai tafi, amma Saul ya kama alkyabbar Sama'ila, sai ta yage.

28. Sai Sama'ila ya ce masa, “Yau Ubangiji ya yage sarautar Isra'ila daga gare ka. Ya ba da ita ga maƙwabcinka wanda ya fi ka.

29. Gama Maɗaukaki na Isra'ila ba zai yi ƙarya, ko ya sāke nufinsa ba. Shi ba mutum ba ne, da zai sāke nufinsa.”

30. Sai Saul ya ce, “Na yi zunubi, amma duk da haka ka darajanta ni a gaban shugabannin mutanena, da gaban Isra'ilawa, ka zo, mu tafi tare domin in yi wa Ubangiji Allah sujada.”

31. Sama'ila kuwa ya tafi tare da Saul, Saul kuwa ya yi wa Ubangiji sujada.

32. Sa'an nan Sama'ila ya ce, “Ku kawo mini Agag Sarkin Amalekawa.” Sai Agag ya taho wurinsa, yana rawar jiki don tsoro, yana cewa a ransa, “Hakika, azabar mutuwa ta fi ɗaci.”

33. Sama'ila ya ce masa, “Kamar yadda takobinka ya mai da mata marasa 'ya'ya, haka za a mai da mahaifiyarka ta zama marar ɗa.” Sai Sama'ila ya sassare Agag gunduwa gunduwa a gaban bagade a Gilgal.

34. Sa'an nan Sama'ila ya tafi Rama, Saul kuwa ya tafi gidansa a Gibeya.

35. Daga ran nan Sama'ila bai ƙara saduwa da sarki Saul ba, har rasuwar Sama'ila, amma ya ji juyayin Saul. Ubangiji kuwa bai ji daɗi da ya sa Saul ya zama Sarkin Isra'ila ba.

Karanta cikakken babi 1 Sam 15