Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 15:23-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Gama tayarwa kamar zunubin bokanci take. Taurinkai kuma kamar bautar gumaka yake. Kamar yadda ka ƙi umarnin Ubangiji, haka nan shi ma ya ƙi ka da zama sarki.”

24. Sa'an nan Saul ya ce wa Sama'ila, “Na yi zunubi, na yi rashin biyayya ga umarnin Ubangiji da kuma koyarwarsa. Na ji tsoron mutanena, na kuwa biye wa abin da suke so.

25. Yanzu fa, ina roƙonka ka gafarta mini zunubina, ka koma tare da ni domin in yi wa Ubangiji sujada.”

26. Sama'ila ya ce wa Saul, “Ba zan tafi tare da kai ba, gama ka ƙi umarnin Ubangiji, Ubangiji kuwa ya ƙi ka da zama Sarkin Isra'ila.”

27. Sa'an nan Sama'ila ya juya zai tafi, amma Saul ya kama alkyabbar Sama'ila, sai ta yage.

28. Sai Sama'ila ya ce masa, “Yau Ubangiji ya yage sarautar Isra'ila daga gare ka. Ya ba da ita ga maƙwabcinka wanda ya fi ka.

29. Gama Maɗaukaki na Isra'ila ba zai yi ƙarya, ko ya sāke nufinsa ba. Shi ba mutum ba ne, da zai sāke nufinsa.”

30. Sai Saul ya ce, “Na yi zunubi, amma duk da haka ka darajanta ni a gaban shugabannin mutanena, da gaban Isra'ilawa, ka zo, mu tafi tare domin in yi wa Ubangiji Allah sujada.”

31. Sama'ila kuwa ya tafi tare da Saul, Saul kuwa ya yi wa Ubangiji sujada.

Karanta cikakken babi 1 Sam 15