Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 15:14-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Sama'ila ya ce masa, “To, ina baicin wannan kukan shanu da na tumaki da nake ji?”

15. Saul kuwa ya ce, “Ai, mutanena ne suka kawo su daga Amalekawa. Gama sun bar mafi kyau na tumaki, da na shanu domin su miƙa su sadaka ga Ubangiji Allahnka. Mun hallaka sauran ƙaƙaf.”

16. Sa'an nan Sama'ila ya ce wa Saul, “Dakata, in faɗa maka abin da Ubangiji ya faɗa mini a daren jiya.” Sai Saul ya ce, “Faɗa mini.”

17. Sama'ila ya ce, “Ko da yake kana ganin kanka kai ba wani abu ne ba, ashe, ba kai ne yanzu shugaban kabilan Isra'ila ba? Ubangiji ya sa ka zama Sarkin Isra'ila,

18. ya kuma umarce ka ka tafi ka hallakar da waɗannan mugayen mutane, wato Amalekawa. Ya faɗa maka ka yi yaƙi, har ka hallaka su ƙaƙaf, kada ka rage ko guda ɗaya.

19. Me ya sa ba ka yi biyayya da shi ba? Don me ka fāɗa wason ganima, ka yi abin da Ubangiji ba ya so?”

20. Sai Saul ya amsa wa Sama'ila, ya ce, “Na yi wa Ubangiji biyayya, gama na tafi kamar yadda ya faɗa mini, na kamo sarki Agag, na kuma hallaka Amalekawa ƙaƙaf.

21. Amma mutanena ba su kashe tumaki da shanu mafi kyau ba, amma suka kawo su domin sadaka ga Ubangiji Allahnka a Gilgal.”

22. Sai Sama'ila ya ce, “Me Ubangiji ya fi so? Biyayya, ko kuwa sadakoki da hadayu? Ya fi kyau a yi masa biyayya, da a miƙa masa hadayar tumaki mafi kyau.

Karanta cikakken babi 1 Sam 15