Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 15:1-10-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sama'ila ya ce wa Saul, “Ubangiji ya aike ni in zuba maka man keɓewa don ka zama sarkin mutanensa, Isra'ila. Yanzu sai ka yi biyayya da maganar Ubangiji.

2. Zai hukunta Amalekawa saboda sun yi gāba da Isra'ilawa lokacin da suke tahowa daga Masar.

3. Ka tafi yanzu, ka fāɗa wa Amalekawa da yaƙi. Ka hallakar da dukan abin da suke da shi. Kada ka rage kome, ka karkashe su dukka, da mata da maza, da yara da jarirai, da takarkarai, da tumaki, da raƙuma, da jakai.”

4. Saul kuwa ya kira mutanen da ya ƙidaya a Telem, sojoji dubu ɗari biyu (200,000) daga Isra'ila, da dubu goma (10,000) daga Yahuza.

5. Sa'an nan Saul ya zo birnin Amalekawa ya yi kwanto a cikin kwari.

6. Ya ce wa Keniyawa, “Ku tafi, ku rabu da Amalekawa, don kada in hallaka ku tare da su, gama kun yi wa dukan Isra'ilawa karamci lokacin da suka fito daga Masar.” Keniyawa kuwa suka fita daga cikin Amalekawa.

7. Saul ya ci Amalekawa, tun daga Hawila har zuwa Shur, da yake gabashin Masar,

8. ya kama Agag Sarkin Amalekawa da rai, ya hallaka mutane ƙaƙaf da takobi.

9. Amma Saul da jama'arsa suka bar Agag da rai, ba su kuma kashe tumaki da takarkarai mafi kyau ba, da 'yan maruƙa, da raguna, da dukan abin da yake mai kyau, bai yarda su hallaka su duka ba, amma sun hallaka dukan abin da yake rainanne ko marar amfani.

10-11. Sai Ubangiji ya yi magana da Sama'ila ya ce, “Na yi baƙin ciki da na sa Saul ya zama sarki, gama ya rabu da ni, ya yi rashin biyayya ga umarnaina,” Sama'ila kuwa ya yi fushi, ya yi ta roƙo ga Ubangiji dukan dare.

Karanta cikakken babi 1 Sam 15