Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 14:28-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Sai wani daga cikin jama'a ya ce, “Ai, mahaifinka ya yi wa mutane barazana da rantsuwa cewa, ‘La'ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin faɗuwar rana.’ ” Mutane kuwa suka tafke.

29. Jonatan kuwa ya ce, “Lalle mahaifina ya wahalar da jama'a! Dubi yadda na wartsake sa'ad da na ɗanɗana 'yar zuman nan.

30. Da yaya zai zama yau da a ce mutane sun ci abinci sosai daga ganimar abokan gābansu, wadda suka samo! Ai, da kisan da aka yi wa Filistiyawa ya fi haka.”

31. Filistiyawa sun sha ɗibga a wannan rana, tun daga Mikmash har zuwa Ayalon. Isra'ilawa suka tafke da yunwa.

32. Sai suka yi warwason ganima, suka kwashe tumaki, da shanu, da maruƙa, suka yanyanka su, suka ci naman ɗanye.

33. Sai aka faɗa wa Saul, “Ga shi, mutane suna yi wa Ubangiji laifi, suna cin nama ɗanye.”Saul kuwa ya ce, “Kun ci amana. Ku mirgino babban dutse a nan wurina.”

34. Sa'an nan ya ce, “Ku tafi ku faɗa wa jama'a duka, su kawo takarkarai da tumaki a nan, su yanyanka su, su ci a nan, don kada su yi wa Ubangiji zunubi da cin nama ɗanye.” Sai dukansu suka kawo takarkaransu a wannan dare, suka yanyanka a wurin.

35. Saul kuwa ya gina wa Ubangiji bagade. Shi ne bagade na farko da ya gina wa Ubangiji.

Karanta cikakken babi 1 Sam 14