Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 14:20-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Sa'an nan Saul da mutanen da suke tare da shi suka taru, suka tafi su yi yaƙi. Sai suka tarar Filistiyawa sun ruɗe suna ta yaƙi da junansu. Aka yi babbar yamutsewa.

21. Ibraniyawan da suke tare da Filistiyawa a dā, waɗanda suka bi su zuwa sansani, suka koma wajen Isra'ilawan da suke tare da Saul da Jonatan.

22. Waɗanda kuma suka bi ta ƙasar tudu ta Ifraimu, da suka ji labari Filistiyawa suna gudu, suka fito suka fafare su.

23. Haka Ubangiji ya ceci Isra'ilawa a ranan nan. Yaƙin kuwa ya kai har gaba da Bet-awen.

24. A ran nan kuwa Isra'ilawa sun sha wahala, gama Saul ya yi rantsuwa mai ƙarfi ya ce, “La'ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin faɗuwar rana tun ban ɗauko fansa a kan abokan gābana ba.” Don haka ba mutumin da ya ɗanɗana abinci.

25-26. Da dukan mutane suka shiga kurmi, sai ga zuma ko'ina, amma ba wanda ya lakata da yatsa ya sa a baka, domin mutane suna tsoron la'anar Saul.

27. Amma Jonatan bai ji barazanar da mahaifinsa ya yi wa jama'a ba, sai ya lakaci saƙar zuma da kan sandansa ya sa a hannu ya kai baka, sa'an nan idanunsa suka buɗe.

Karanta cikakken babi 1 Sam 14