Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 13:14-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Amma yanzu sarautarka ba za ta tabbata ba, gama Ubangiji ya riga ya sami mutum wanda yake so. Ubangiji ya riga ya naɗa shi ya zama sarkin jama'arsa, domin ba ka kiyaye umarnin Ubangiji ba.”

15. Sama'ila ya tashi daga Gilgal zuwa Gibeya ta Biliyaminu. Da Saul ya ƙidaya mutanen da suke tare da shi, ya tarar wajen mutum ɗari shida ne.

16. Sai Saul da ɗansa, Jonatan, da mutanen da suke tare da su suka zauna a Geba ta Biliyaminu. Filistiyawa kuwa suka kafa sansaninsu a Mikmash.

17. Sai runduna uku na mahara suka fito daga sansanin Filistiyawa. Runduna ɗaya ta nufi Ofra, zuwa ƙasar Shuwal.

18. Runduna guda kuma ta nufi Bet-horon, guda kuwa ta nufi iyakar da take fuskantar kwarin Zeboyim wajen jeji.

19. A wannan lokaci ba maƙeri a ƙasar Isra'ila duka, domin Filistiyawa sun hana Ibraniyawa su ƙera wa kansu takuba ko māsu.

20. Saboda haka kowane Ba'isra'ile yakan gangara zuwa Filistiyawa domin ya koɗa bakin garmarsa, da fartanyasa, da gatarinsa, da laujensa,

21. duk lokacin da za su koɗar bakin garma da fartanya sai su biya sulusin shekel ne, ladan koɗar gatari da shirya abin korar shanun noma sulusin shekel ne.

22. A ranar da yaƙi ya tashi, ba a sami wanda yake da takobi ko mashi ba a cikin mutanen da suke tare da Saul da Jonatan. Amma Saul da ɗansa, Jonatan, suna da su.

23. Sai ƙungiyar sojojin Filistiyawa ta fita zuwa mashigin Mikmash.

Karanta cikakken babi 1 Sam 13