Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 11:8-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Sa'ad da Saul ya tara mutane a Bezek, aka sami mutum dubu ɗari uku (300,000) daga Isra'ila, dubu talatin (30,000) kuma daga Yahuza.

9. Suka faɗa wa manzannin da suka zo. “Ga abin da za ku faɗa wa mutanen Yabesh, ‘Gobe, kafin rana ta yi zafi, za ku sami ceto.’ ” Sa'ad da manzannin suka je, suka faɗa wa mutanen Yabesh saƙon, suka yi murna.

10. Saboda haka mutanen Yabesh suka ce wa Nahash Ba'ammone, “Gobe za mu zo wurinku, ka yi mana yadda ka ga dama.”

11. Gari na wayewa, sai Saul ya raba mutanen kashi uku, suka fāɗa wa sansanin Ammonawa da kisa tun da sassafe har rana tsaka, aka warwatsa waɗanda suka tsira ɗaya ɗaya.

12. Jama'ar Isra'ila kuwa suka ce wa Sama'ila, “Su wa suka ce Saul ba zai sarauce mu ba? Ka kawo su, mu kashe su.”

Karanta cikakken babi 1 Sam 11