Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Saul Ya Ci Ammonawa

1. Sai Nahash Ba'ammone ya kewaye Yabesh da yaƙi. Dukan mutanen Yabesh kuwa suka ce masa, “Ka ƙulla amana da mu, mu kuwa za mu bauta maka.”

2. Nahash Ba'ammone kuwa ya ce, “Zan ƙulla amana da ku a kan wannan sharaɗi, wato in ƙwaƙule idanunku na dama don ku zama abin raini ga Isra'ilawa.”

3. Dattawan Yabesh kuwa suka ce masa, “Ka ba mu zarafi kwana bakwai domin mu aika da manzanni a dukan ƙasar Isra'ila, idan ba mu sami wanda zai cece mu ba, to, sai mu ba da kanmu gare ku.”

4. Da manzannin suka zo Gibeya inda Saul yake, suka ba mutane labarin abin da ya faru. Sai jama'a duka suka yi kuka.

5. Saul kuwa yana dawowa daga gona ke nan, tare da shanunsa na huɗa. Sai ya ce, “Me ya sami jama'a suke kuka haka?” Suka faɗa masa labarin mutanen Yabesh.

6. Da Saul ya ji, sai Ruhun Ubangiji ya sauko a kansa da iko, ya husata ƙwarai.

7. Ya kwance shanun, ya yanka gunduwa gunduwa, ya aika da su ko'ina a ƙasar Isra'ila ta hannun manzanni, yana cewa, “Duk wanda bai fito ya bi Saul da Sama'ila ba, to, haka za a yi da shanun nomansa!”Jama'a suka ji tsoron abin da Ubangiji zai yi, suka fita gaba ɗaya kamar mutum guda.

8. Sa'ad da Saul ya tara mutane a Bezek, aka sami mutum dubu ɗari uku (300,000) daga Isra'ila, dubu talatin (30,000) kuma daga Yahuza.

9. Suka faɗa wa manzannin da suka zo. “Ga abin da za ku faɗa wa mutanen Yabesh, ‘Gobe, kafin rana ta yi zafi, za ku sami ceto.’ ” Sa'ad da manzannin suka je, suka faɗa wa mutanen Yabesh saƙon, suka yi murna.

10. Saboda haka mutanen Yabesh suka ce wa Nahash Ba'ammone, “Gobe za mu zo wurinku, ka yi mana yadda ka ga dama.”

11. Gari na wayewa, sai Saul ya raba mutanen kashi uku, suka fāɗa wa sansanin Ammonawa da kisa tun da sassafe har rana tsaka, aka warwatsa waɗanda suka tsira ɗaya ɗaya.

12. Jama'ar Isra'ila kuwa suka ce wa Sama'ila, “Su wa suka ce Saul ba zai sarauce mu ba? Ka kawo su, mu kashe su.”

13. Amma Saul ya ce, “Ba wanda za a kashe a yau, gama Ubangiji ya yi wa Isra'ila ceto a yau.”

14. Sai Sama'ila ya ce wa jama'a, “Ku zo, mu tafi Gilgal a yi wankan sarautar a can.”

15. Jama'a duka kuwa suka nufi Gilgal, suka yi wa Saul wankan sarauta a gaban Ubangiji. Suka kuma miƙa wa Ubangiji hadaya ta salama. A can kuwa Saul tare da dukan mutanen Isra'ila suka yi murna ƙwarai.