Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 1:17-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Sai Eli ya ce mata, “Ki sauka lafiya, Allah na Isra'ila ya amsa miki roƙonki.”

18. Ita kuma ta amsa, ta ce, “Bari baiwarka ta sami tagomashi a gare ka.” Sa'an nan ta tafi, ta ci abinci. Ba ta ƙara ɓata ranta ba.

19. Elkana da iyalinsa suka tashi tun da sassafe suka yi wa Ubangiji sujada, sa'an nan suka koma gidansu a Rama. Elkana fa ya kwana da matarsa, Hannatu. Ubangiji kuwa ya tuna da ita.

20. Ta yi juna biyu, ta haifa ɗa, ta raɗa masa suna Sama'ila, wato “Na roƙo shi daga wurin Ubangiji.”

21. Elkana da iyalinsa duka suka tafi Shilo domin su miƙa wa Ubangiji hadaya ta shekara shekara, ya kuma cika wa'adinsa.

22. Amma Hannatu ba ta tafi ba, sai ta ce wa mijinta, “Da zarar an yaye yaron, zan kai shi domin ya zauna a gidan Ubangiji muddin ransa.”

23. Elkana ya ce mata, “Ki yi abin da kika ga ya fi kyau, ki jira har ki yaye shi, Ubangiji dai ya cika maganarsa.” Hannatu ta tsaya a gida, ta yi ta renon ɗanta.

24. Sa'ad da ta yaye yaron, sai ta ɗauke shi, ta kuma ɗauki bijimi bana uku, da mudun gari, da salkar ruwan inabi, ta kai shi ɗakin Ubangiji a Shilo, yaron kuwa yana ɗan ƙarami.

25. Sai suka yanka bijimin, suka kuma kai yaron wurin Eli.

26. Sa'an nan Hannatu ta ce, “Gafara dai, ba ka tuna da ni ba? Ai, ni ce matar da ta taɓa tsayawa a gabanka, tana roƙon Ubangiji.

27. Na roƙi Ubangiji wannan yaro, Ubangiji kuwa ya biya mini bukatata da na roƙa a gare shi.

28. Saboda haka nake miƙa shi ga Ubangiji muddin ransa. Ya zama na Ubangiji.”A can ya yi wa Ubangiji sujada.

Karanta cikakken babi 1 Sam 1