Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yak 3:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya ku 'yan'uwana, kada yawancinku su zama masu koyarwa, domin kun sani, mu da muke koyarwa za a yi mana shari'a da ƙididdiga mafi tsanani.

2. Domin dukanmu muna yin kuskure da yawa. In kuwa mutum ba ya shirme a maganarsa, to, shi cikakken mutum ne, yana kuwa iya kame duk sauran gaɓoɓinsa ma.

3. Ga misali, idan mun sa linzami a bakin doki, don mu bi da shi, mukan sarrafa dukan jikinsa ma.

4. Ku dubi jiragen ruwa kuma, ko da yake suna da girma haka ƙaƙƙarfar iska kuma tana kora su, duk da haka, da ɗan ƙaramin ƙarfe ne matuƙi yake juya su duk inda ya nufa.

5. Haka ma harshe yake, ga shi, ɗan ƙaramin abu ne, sai manyan fariya! Ku dubi yadda ɗan ƙaramin ƙyastu yake kunna wa babban jeji wuta!

6. Harshe ma wuta ne fa! A cikin duk gaɓoɓinmu, harshe shi ne tushen kowace irin mugunta, mai ɓata dukan jiki, mai zuga zuciyar mutum ta tafasa, shi kuwa Gidan Wuta ne yake zuga shi.

7. Don kuwa ana iya sarrafa kowace irin dabba, da tsuntsu, da masu jan ciki, da halittar ruwa, ɗan adam har yā sarrafa su ma,

8. amma ba ɗan adam ɗin da zai iya sarrafa harshe, ai, mugunta ne da ba ta hanuwa, a cike yake da dafi mai kashewa.

9. Da shi muke yabon Ubangiji Uba, da shi kuma muke zagin mutane waɗanda aka halitta da kamannin Allah.

10. Da baki ɗaya ake yabo, ake kuma zagi. 'Yan'uwana, ai, wannan bai kamata ba!

11. Ashe, marmaro ɗaya ya iya ɓuɓɓugowa da ruwan daɗi da na zartsi ta ido guda?

Karanta cikakken babi Yak 3