Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yak 1:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Daga Yakubu, bawan Allah, da kuma na Ubangiji Yesu Almasihu, zuwa ga kabilan nan goma sha biyu da suke a warwatse a duniya. Gaisuwa mai yawa.

2. Ya ku 'yan'uwana, duk sa'ad da gwaje-gwaje iri iri suka same ku, ku mai da su abin farin ciki ƙwarai.

3. Domin kun san jarrabawar bangaskiyarku takan haifi jimiri.

4. Sai kuma jimiri ya yi cikakken aikinsa, domin ku zama kamilai cikakku kuma, ba ku gaza da kome ba.

5. In waninku ya rasa hikima, sai ya roƙi Allah, mai ba kowa hannu sake, ba tare da gori ba, sai kuwa a ba shi.

6. Amma fa sai ya roƙa da bangaskiya, ba tare da shakka ba. Don mai shakka kamar raƙuman ruwan teku yake, waɗanda iska take korawa tana tuttunkuɗawa.

7-8. Kada irin mutumin nan mai zuciya biyu, wanda bai tsai da zuciyarsa a gu ɗaya a dukan al'amuransa ba, ya sa rai da wani abu a gun Ubangiji.

9. Ƙasƙantaccen ɗan'uwa yă yi taƙama da ɗaukakarsa.

10. Mai arziki kuma yă yi alfarma da ƙasƙancinsa, gama zai shuɗe kamar hudar ciyawa.

11. In rana ta tāke da ƙunarta, sai ciyawa ta bushe, hudarta ta kaɗe, kyanta kuma ya gushe. Haka ma mai arziki zai gushe yana a cikin tsakiyar harkarsa.

Karanta cikakken babi Yak 1