Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 8:32-51 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. Za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta 'yanta ku.”

33. Suka amsa masa suka ce, “Ai, mu zuriyar Ibrahim ne, ba mu taɓa bauta wa kowa ba. Yaya kuma za ka ce za a 'yanta mu?”

34. Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, duk mai aikata zunubi bawan zunubi ne.

35. Ai, bawa ba ya ɗorewa a gida har abada, ɗa kuwa yana ɗorewa.

36. In kuwa Ɗan ya 'yanta ku, za ku 'yantu, 'yantuwar gaske.

37. Na san dai ku zuriyar Ibrahim ne, amma kuwa kuna neman kashe ni, don maganata ba ta shigarku.

38. Ina faɗar abin da na gani a wurin Ubana, ku kuma kuna yin abin da kuka ji daga wurin naku uba.”

39. Suka amsa masa suka ce, “Ai, Ibrahim ne ubanmu.” Yesu ya ce musu, “Da ku 'ya'yan Ibrahim ne, da sai ku yi aikin da Ibrahim ya yi.

40. Ga shi yanzu, kuna neman kashe ni, ni mutumin da na gaya muku gaskiyar da na ji wurin Allah. Ba haka Ibrahim ya yi ba.

41. Ku kuna aikin da ubanku yake yi ne.” Suka ce masa, “Ba a haife mu daga fasikanci ba, ubanmu ɗaya ne, wato Allah.”

42. Yesu ya ce musu, “Da Allah ne Ubanku da kun ƙaunace ni, domin daga wurin Allah na fito, ga ni nan kuwa. Ban zo domin kaina ba, shi ne ya aiko ni.

43. Don me ba kwa gane maganata? Don ba kwa iya jimirin jin maganata ne.

44. Ku na ubanku Iblis ne, niyyarku kuwa ku aikata burin ubanku. Shi dā ma tun farko mai kisankai ne, bai zauna kan gaskiya ba, don ba ruwansa da gaskiya. Duk sa'ad da yake ƙarya, cinikinsa yake yi, don shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma.

45. Amma domin ina faɗar gaskiya, ba kwa gaskata ni.

46. A cikinku wa zai iya haƙƙaƙewa na taɓa yin zunubi? In kuwa gaskiya nake faɗa, to, don me ba kwa gaskata ni?

47. Na Allah yakan saurari Maganar Allah. Abin da ya sa ba kwa sauraronta ke nan, don ku ba na Allah ba ne.”

48. Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Ashe, gaskiyarmu da muka ce kai Basamariye ne, kana kuma da iska.”

49. Yesu ya amsa ya ce, “Ni ba mai iska ba ne. Ubana nake girmamawa, ku kuwa wulakanta ni kuke yi.

50. Ba ni nake nemar wa kaina girma ba, akwai mai nemar mini, shi ne kuma mai yin shari'a.

51. Lalle hakika, ina gaya muku, kowa ya kiyaye maganata ba zai mutu ba har abada.”

Karanta cikakken babi Yah 8