Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 7:39-53 Littafi Mai Tsarki (HAU)

39. To, wannan shi ne ya faɗa game da Ruhu, wanda masu gaskatawa da shi za su karɓa, domin har yanzu ba a ba da Ruhu ba, saboda ba a ɗaukaka Yesu ba tukuna.

40. Da jin maganan nan waɗansu daga cikin taron suka ce, “Hakika wannan annabin nan ne.”

41. Waɗansu kuwa suka ce, “Wannan Almasihu ne.” Amma waɗansu suka ce, “Me? Ashe, Almasihu daga ƙasar Galili zai fito?

42. Nassi ba cewa ya yi Almasihu zuriyar Dawuda ne ba, daga kuma Baitalami yake, ƙauyen da Dawuda ya zauna?”

43. Sai kuma rabuwa ta shiga tsakaninsu a kansa.

44. Waɗansunsu suka so su kama shi, amma ba wanda ya taɓa shi.

45. Daga nan dogaran Haikali suka koma wurin manyan firistoci da Farisiyawa, su kuwa suka ce musu, “Don me ba ku kawo shi ba?”

46. Sai dogaran suka amsa suka ce, “A'a, ba mutumin da ya taɓa magana kamar wannan!”

47. Sai Farisiyawa suka amsa musu suka ce, “Af! Har ku ma an ɓad da ku ne?

48. Ashe, akwai wani daga cikin shugabanni ko Farisiyawa da ya gaskata da shi?

49. Amma wannan taro da ba su san Attaura ba, ai, la'anannu ne.”

50. Nikodimu kuwa da ya je wurinsa dā, yana kuwa ɗaya daga cikinsu, ya ce musu,

51. “Ashe, shari'armu takan hukunta mutum tun ba a ji daga bakinsa ba, an kuma san abin da yake ciki?”

52. Suka amsa masa suka ce, “Kai ma Bagalile ne? Bincika mana ka gani, ai, ba wani annabi da zai bayyana a ƙasar Galili.”[

53. Sai kowa ya tafi gida.

Karanta cikakken babi Yah 7