Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 7:3-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Sai 'yan'uwansa suka ce masa, “Tashi daga nan mana ka tafi ƙasar Yahudiya, almajiranka su ma su ga ayyukan da kake yi.

4. Ai, ba mai aiki a ɓoye in yana so ya shahara. Tun da yake kana yin waɗannan al'amura, to, sai ka bayyana kanka ga duniya.”

5. Domin ko dā ma 'yan'uwansa ba su gaskata da shi ba.

6. Sai Yesu ya ce musu, “Lokacina bai yi ba tukuna, amma ku, koyaushe lokacinku ne.

7. Ba dama duniya ta ƙi ku, amma ni take ƙi, don na shaide ta a kan ayyukanta mugaye ne.

8. Ku dai ku tafi idin. Ni ba za ni ba yanzu, don lokacina bai yi sosai ba tukuna.”

9. Da ya faɗa musu haka, ya dakata a ƙasar Galili.

10. Bayan 'yan'uwansa sun tafi idin kuwa, shi ma ya tafi, amma a ɓoye, ba a fili ba.

11. Yahudawa suna ta nemansa a wurin idin suna cewa, “Ina yake ne?”

12. Taro kuma suka riƙa maganarsa a raɗe, waɗansu na cewa, “Mutum ne nagari.” Waɗansu kuma na cewa, “A'a, ai, ɓad da jama'a yake.”

13. Amma ba wanda ya yi magana tasa a fili don tsoron Yahudawa.

14. Wajen tsakiyar idin sai Yesu ya shiga Haikali ya koyar.

15. Yahudawa suka yi mamakin abin, suka ce, “Yaya mutumin nan yake da karatu haka, ga shi kuwa, bai taɓa koyo ba?”

16. Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Koyarwata ba tawa ba ce, ta wanda ya aiko ni ce.

17. Duk mai son aikata nufin Allah zai san koyarwan nan ko ta Allah ce, ko domin kaina nake faɗa.

18. Mai magana don kansa, neman ɗaukakar kansa yake yi. Amma mai neman ɗaukakar wanda ya aiko shi, shi ne mai gaskiya, ba kuwa rashin gaskiya a gare shi.

19. Ashe, ba Musa ne ya ba ku Shari'a ba? Duk da haka ba mai kiyaye Shari'ar a cikinku. Don me kuke neman kashe ni?”

Karanta cikakken babi Yah 7