Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 6:6-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ya faɗi haka ne fa domin ya gwada shi, saboda shi kansa ya san abin da zai yi.

7. Filibus ya amsa ya ce, “Ai, ko gurasar dinari metan ma ba ta isa ko wannensu ya sami kaɗan ba.”

8. Sai Andarawas ɗan'uwan Bitrus ɗaya daga cikin almajiransa, ya ce masa,

9. “Ga wani ɗan yaro nan da gurasa biyar na sha'ir, da kuma kifi biyu. Amma me waɗannan za su yi wa mutane masu yawa haka?”

10. Yesu ya ce, “Ku ce wa mutane su zauna.” Wuri ne kuwa mai ciyawa. Sai mazaje suka zazzaune, su wajen dubu biyar.

11. Yesu ya ɗauki gurasar, bayan ya yi godiya ga Allah kuma, sai ya rarraba wa waɗanda suke zazzaune. Haka kuma ya yi da kifin, gwargwadon abin da ya ishe su.

12. Da suka ci suka ƙoshi, sai ya ce wa almajiransa, “Ku tattara gutsattsarin da suka saura, kada kome ya ɓata.”

13. Sai suka tattara gutsattsarin gurasar nan biyar na sha'ir da suka saura bayan kowa ya ci, suka cika kwando goma sha biyu.

14. Da jama'a suka ga mu'ujizar da ya yi, suka ce, “Lalle, wannan shi ne annabin nan mai zuwa duniya.!”

15. Da Yesu ya gane suna shirin zuwa su ɗauke shi ƙarfi da yaji su naɗa shi sarki, sai ya sāke komawa kan dutsen shi kaɗai.

16. Da magariba ta yi, sai almajiransa suka gangara teku.

17. Suka shiga jirgi suka tasar wa haye tekun zuwa Kafarnahun. A sa'an nan duhu ya yi, Yesu kuwa bai zo wurinsu ba tukuna.

18. Sai tekun ta fara hauka saboda wata riƙaƙƙiyar iska da take busowa.

19. Bayan sun yi tuƙi wajen mil uku ko huɗu, sai suka hango Yesu yana tafiya a kan ruwan, ya kusato jirgin. Sai suka firgita.

20. Amma ya ce musu, “Ni ne, kada ku ji tsoro.”

Karanta cikakken babi Yah 6