Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 6:24-39 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Sa'ad da kuwa taron suka ga ba Yesu, ba almajiransa a nan, su ma suka shiga ƙananan jiragen, suka tafi Kafarnahum neman Yesu.

25. Da suka same shi a hayin tekun, suka ce masa, “Ya Shugaba, yaushe ka zo nan?”

26. Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, kuna nemana ne ba don kun ga mu'ujizai ba, sai don kun ci gurasar nan kun ƙoshi.

27. Kada ku yi wahala a kan neman abinci mai lalacewa, sai dai a kan abinci mai dawwama har ya zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. Domin shi ne wanda Uba, wato Allah, ya tabbatar wa da ikon yin haka.”

28. Sai suka ce masa, “Me za mu yi mu aikata ayyukan da Allah yake so?”

29. Yesu ya amsa musu ya ce, “Wannan shi ne aikin da Allah yake so, wato ku gaskata da wanda ya aiko.”

30. Sai suka ce masa, “To, wace mu'ujiza za ka yi mu gani mu gaskata ka? Me za ka yi?

31. Kakannin kakanninmu sun ci manna a jeji, yadda yake a rubuce cewa, ‘Ya ba su gurasa daga Sama su ci.’ ”

32. Sa'an nan Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, ba Musa ne ya ba ku gurasar nan daga Sama ba, Ubana ne yake ba ku hakikanin Gurasa daga Sama.

33. Ai, Gurasan Allah shi ne mai saukowa daga Sama, mai ba duniya rai.”

34. Sai suka ce masa, “Ya Ubangiji, ka riƙa ba mu irin wannan gurasa kullum!”

35. Yesu ya ce musu, “Ni ne gurasa mai ba da rai. Wanda ya zo gare ni ba zai ji yunwa ba har abada, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada.

36. Na dai gaya muku, kun gan ni, duk da haka ba ku ba da gaskiya ba.

37. Duk wanda Uba ya ba ni zai zo gare ni, wanda kuwa ya zo gare ni ba zan kore shi ba ko kaɗan.

38. Domin na sauko daga Sama, ba domin in bi nufin kaina ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni.

39. Nufin wanda ya aiko ni kuwa, shi ne kada in yar da kowa daga cikin dukkan waɗanda ya ba ni, sai dai in tashe su a ranar ƙarshe.

Karanta cikakken babi Yah 6