Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 5:18-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Don haka, Yahudawa suka ƙara nema su kashe shi, ba don ya keta Asabar kaɗai ba, har ma domin ya ce Allah Ubansa ne, wato, yana daidaita kansa da Allah.

19. Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, Ɗan ba ya yin kome shi kaɗai, sai abin da ya ga Uba yana yi. Domin duk abin da Uban yake yi, haka shi Ɗan ma yake yi.

20. Domin Uban na ƙaunar Ɗan, yana kuma nuna masa duk abin da shi kansa yake yi, har ma zai nuna masa ayyukan da suka fi waɗannan, domin ku yi al'ajabi.

21. Yadda Uba yake ta da matattu ya kuma raya su, haka Ɗan ma yake rayar da wanda ya nufa.

22. Uba ba ya hukunta kowa, sai dai yā danƙa dukkan hukunci ga Ɗan,

23. domin kowa yă girmama Ɗan, kamar yadda ake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi ke nan.

24. Lalle hakika, ina gaya muku, duk mai jin maganata, yake kuma gaskata wanda ya aiko ni, yana da rai madawwami. Ba za a yi masa hukunci ba, domin ya riga ya tsere wa mutuwa, ya kai ga rai.

25. “Lalle hakika, ina gaya muku, lokaci na zuwa, har ma ya yi, da matattu za su ji muryar Ɗan Allah, masu ji kuwa su rayu.

26. Yadda Uba kansa yake tushen rai, haka ya sa Ɗan ya zama tushen rai.

Karanta cikakken babi Yah 5