Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 4:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. To, da Ubangiji Yesu ya sani dai Farisiyawa sun ji labari yana samun almajirai, yana kuma yi musu baftisma fiye da Yahaya

2. (ko da yake dai ba Yesu kansa yake yin baftisma ba, almajiransa ne),

3. sai ya bar ƙasar Yahudiya, ya koma ƙasar Galili.

4. Lalle ne kuwa yă ratsa ƙasar Samariya.

5. Sai ya zo wani gari na ƙasar Samariya, wanda ake kira Saikar, kusa da yankin ƙasar da Yakubu ya ba ɗansa Yusufu.

6. Rijiyar Yakubu kuwa a nan take. Saboda gajiyar tafiya fa, sai Yesu ya zauna haka nan a bakin rijiyar. Wajen tsakar rana ce kuwa.

7. Sai ga wata Basamariya ta zo ɗiban ruwa. Yesu ya ce mata, “Sa mini ruwa in sha.”

8. Almajiransa kuwa sun shiga gari sayen abinci.

9. Sai Basamariyar ta ce masa, “Ƙaƙa kai Bayahude za ka roƙe ni ruwan sha, ni da nake Basamariya?” (Don Yahudawa ba sa cuɗanya da Samariyawa).

10. Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah, da kuma wanda ya ce miki, ‘Sa mini ruwa in sha,’ ai, da kin roƙe shi, shi kuwa zai ba ki ruwan rai.”

Karanta cikakken babi Yah 4