Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 3:22-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Bayan haka, Yesu da almajiransa suka tafi ƙasar Yahudiya. A nan ya jima da su, yana yin baftisma.

23. Yahaya kuma yana yin baftisma a Ainon kusa da Salima, domin da ruwa da yawa a can. Mutane kuwa suka yi ta zuwa ana yi musu baftisma.

24. Domin a sa'an nan ba a sa Yahaya a kurkuku ba tukuna.

25. Sai fa almajiran Yahaya suka tasar wa wani Bayahude da muhawara a kan maganar tsarkakewa.

26. Suka kuma zo wurin Yahaya, suka ce masa, “Ya shugaba, wanda dā kuke tare a hayin Kogin Urdun, wanda kai kanka ma ka shaida shi, to, ga shi, yana yin baftisma, har kowa da kowa yana zuwa wurinsa.”

27. Sai Yahaya ya amsa ya ce, “Ba mai iya samun kome sai ko an ba shi daga Sama.

28. Ku kanku ma shaiduna ne a kan na ce ba ni ne Almasihu ba, amma an aiko ni ne ni riga shi gaba.

29. Mai amarya shi ne ango. Abokin ango kuwa da yake tsaye, yake kuma sauraron magana tasa, yakan yi farin ciki ƙwarai da jin muryar angon. Saboda haka farin cikin nan nawa ya cika.

30. Shi kam, lalle ne ya riƙa ƙaruwa, ni kuwa in riƙa raguwa.

31. “Mai zuwa daga Sama yana Sama da kowa. Wanda yake na ƙasa asalinsa kuwa na ƙasa ne, maganar ƙasa kuma yake yi. Mai zuwan nan daga Sama yana Sama da kowa.

32. Abin da ya ji, ya kuma gani, shi yake shaidarwa, duk da haka ba wanda yake yarda da shaidarsa.

33. Duk wanda ya yarda da shaidarsa, ya haƙƙaƙe, cewa, Allah mai gaskiya ne.

34. Domin wanda Allah ya aiko, zantuttukan Allah yake faɗa, gama Allah yana ba da Ruhu ba da iyakancewa ba.

35. Uban yana ƙaunar Ɗan, ya kuma sa kome a hannunsa.

36. Wanda ya gaskata da Ɗan, yana da rai madawwami. Wanda ya ƙi bin Ɗan kuwa, ba zai sami rai ba, sai dai fushin Allah ya tabbata a gare shi.”

Karanta cikakken babi Yah 3