Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 3:2-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Wannan mutum ya zo wurin Yesu da dad dare, ya ce masa, “Ya Shugaba, mun sani kai malami ne da ka zo daga wurin Allah, domin ba mai iya yin waɗannan mu'ujizan da kake yi, sai ko Allah yana tare da shi.”

3. Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba a sāke haifar mutum ba, ba zai iya ganin Mulkin Allah ba.”

4. Nikodimu ya ce masa, “Ƙaƙa za a haifi mutum bayan ya tsufa? Wato, ya iya komawa a cikin uwa tasa ta sāke haifo shi?”

5. Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba an haifi mutum ta ruwa da kuma Ruhu ba, ba zai iya shiga Mulkin Allah ba.

6. Abin da mutum ya haifa mutum ne, abin kuma da Ruhu ya haifa ruhu ne.

7. Kada ka yi mamaki domin na ce maka, ‘Dole a sāke haifarku.’

8. Iska tana busawa inda ta ga dama. Kakan ji motsinta, amma ba ka san inda ta fito da inda za ta. Haka fa yake ga duk wanda Ruhu ya haifa.”

9. Sai Nikodimu ya amsa masa ya ce, “Ƙaƙa wannan zai yiwu?”

10. Yesu ya amsa masa ya ce, “Ashe, kai ma da kake malamin Isra'ila, ba ka fahimci waɗannan al'amura ba?

11. Lalle hakika, ina gaya maka, abin da muka sani shi muke faɗa, muna kuma shaidar da abin da muka gani, amma kun ƙi yarda da shaidarmu.

12. In na yi muku zancen al'amuran duniya ba ku gaskata ba, yaya za ku gaskata in na yi muku zancen al'amuran sama?

13. Ba wanda ya taɓa hawa cikin Sama sai shi wanda ya sauko daga Sama, wato, Ɗan Mutum da yake Sama.

14. Kamar yadda Musa ya ɗaga macijin nan a jeji, haka kuma dole ne a ɗaga Ɗan Mutum,

15. domin duk wanda ya gaskata da shi, ya sami rai madawwami.

16. “Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami.

17. Gama Allah bai aiko Ɗansa duniya domin yă yanke mata hukunci ba, sai dai domin duniya ta sami ceto ta wurinsa.

18. Duk wanda ya gaskata da shi, ba za a yi masa hukunci ba. Wanda kuwa bai ba da gaskiya ba, an riga an yi masa hukunci, domin bai gaskata da sunan makaɗaicin Ɗan Allah ba.

Karanta cikakken babi Yah 3