Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 21:13-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sai Yesu ya zo ya ɗauki gurasar, ya ba su, haka kuma kifin.

14. Wannan ne fa zuwa na uku da Yesu ya bayyana ga almajiran bayan an tashe shi daga matattu.

15. Da suka karya kumallo Yesu ya ce wa Bitrus, “Bitrus ɗan Yahaya, ka fi waɗannan ƙaunata?” Ya ce masa, “I, ya Ubangiji, ka dai sani ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka yi kiwon 'ya'yan tumakina.”

16. Ya sāke faɗa masa, faɗa ta biyu, “Bitrus ɗan Yahaya, kana ƙaunata?” Ya ce masa, “I, ya Ubangiji, ka dai sani ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka kiyaye tumakina.”

17. Yesu ya faɗa masa, faɗa ta uku, “Bitrus ɗan Yahaya, kana sona?” Sai Bitrus ya yi baƙin ciki don a faɗar nan ta uku ya ce masa, “Kana sona?” Shi kuwa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ai, ka san kome duka, ka kuwa sani ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka yi kiwon tumakina.”

18. Lalle hakika, ina gaya maka, lokacin samartakarka kakan yi wa kanka ɗamara, ka tafi inda ka nufa, amma in ka tsufa, za ka miƙe hannuwanka, wani ya yi maka ɗamara, ya kai ka inda ba ka nufa ba.”

19. (Ya faɗi wannan ne yana kwatanta irin mutuwar da Bitrus zai yi ya ɗaukaka Allah.) Bayan ya faɗi haka, ya ce masa, “Bi ni.”

Karanta cikakken babi Yah 21